Taron kungiyar kawancen NATO a Amurka
May 20, 2012A taron kolin kasashe masu manyan masana'antu na G8 shugabanin kasashe masu mahimmanci a fanin tattalin arziki da Rasha sun cimma matsaya na su hada kai wajen bunkasa yawan abunda kasa kan samu kowace shekara su kuma gudanar da abubuwan da suka shafi kasafin kudin kasashensu a bayyane.
A sakamakon hakan ne ma kasashen da suka halarci taron kolin suka yanke shawarar cewa, kamata yayi Girka ta cigaba da kasancewa cikin rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa yanzu kasashen na Turai na da damammaki da yawa na ganin sun hada kai dan cimma matsaya mai amfani a gare su.
"Wannan ya kunshi abubuwa biyu wadanda suka hada da samar da tallafi da kuma inganta abubuwan da kasa ke sarrfawa kowace shekara domin abubuwa ne da ba za'a iya raba su ba kuma ba zasu iya kalubalantar juna ba"
Merkel ta sake ganawa bayan taron kolin da shugaban Amurka, Barack Obama domin tattauna hanyoyin da kasashen biyu zasu kulla dangantakar taimakawa juna. A daidai lokacin da ake kammala taron na G8, ake sake bude taron kungiyar kawancen tsaron NATO a birnin Chicago na kasar Amurka inda ake tattauna janyewar dakarun kungiyar hadakar daga Afghanistan a karshen shekara ta 2014 da ma yiwuwar girka garkuwar nan na musamman na kare makamai masu linzami a Turai.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal