Taron kwamitin sulhu kan rikicin Gabas ta Tsakiya
May 14, 2021A wannan Jumma'a ce, ya kamata a kwamitin sulhu na MDD ya yi taronsa na gagawa bisa bukatar da wasu kasashe 10 daga cikin mimbobin kwamitin ciki har da Jamhuriyar Nijar da Faransa da Birtaniya suka shigar. Sai dai Amirka ta yi fatali da kiran taron tana mai fatan gudanar da shi a makon gobe.
Wata majiyar diflomasiya ta shaida cewa, ana sa ran taron ya gudana a wannan Lahadi, da zummar duba rikici da ke ci gaba da ta'azzara, wanda ya zuwa yanzu ya halaka fiye da Falasdinawa 100 ciki har da kanana yara, a yayin da Isra'ila ta ce an kashe mata 'yan kasa 7.
Ko a sanyin safiyar yau, rundunar sojin Isra'ila ta musanta kutsawa yankin Falasdinawa na Zirin Gaza a wannan Jumma'a, sa'o'i biyu bayan da aka ambato cewar sojojinta na sama da na kasa sun keta iyakar Gaza a ci gaba da dauki ba dadin da mayakan Hamas.