Taron ministocin EU kan Girka da Spain
May 14, 2012A yau Litinin (14. 05.2012) ne ministocin kuɗin ƙungiyar Tarayyar Turai ke gudanar da taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam domin duba halin da nke wakana a ƙasashen Girka da Spain. A baya ga haka za su kuma tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ba da ƙarin muƙamai cikinsu har da na shugaban ƙasashen ƙungiyar. A dai ƙarshen watan Yuni mai zuwa ne firaminstan Luxembourg, Jean Claude Junker zai cika wa'adin aikin a matsayinsa na shugaban ƙungiyar ministocin kuɗin ƙasashen Turai da ke amani da takardar kuɗin Euro a ƙungiyar. Ana dai kallon Wolfgang Schaeuble, ministan kuɗin Jamus a matsayin wanda zai maye gurbinsa. To amma ko da yake shi kuma ya bayyanar da niyyarsa ta riƙe wannan muƙami, nada shi a matsayin, ya dogara ne akan amincewar sabon zaɓaɓɓen shugaban Faransa, rancois Hollande wanda har yanzu bai bayyanar da matsayinsa game da hakan ba.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh