Taron ministocin harakokin wajen EU a game da rikicin Britania da Iran
March 30, 2007Ministocin harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, na ci gaba da zaman taro a birnin Breme da ke nan ƙasar Jamus.
Ministocin na gudanar da mahaurori a game da saban rikicin da ya ɓarke tsakanin Iran da Britania.
A yammacin yau, ministocin sun hiddo sanarwar bai ɗaya, wadda ta yi Allah wadai da kamun wannan sojojin ruwa Britania, ta kuma bukaci hukumomin Teheran, su yi belins u ba tare da ɓata lokaci ba.
Ministocin sun umurci sakataran harakokin wajen EU Havier Solana, wanda cemma ke bin diddiƙin tantanawar rikicin makaman nuklea, ya gabatarwa Iran, matakin da EU ta ɗauka a game da rikicin wannan sojoji.
Saidai a wani mataki na maida martani, Iran ta buƙaci ƙungiyar gamayyar turai, ta tsame hannuwan ta, kwata-kwata daga rikicin wannan sojoji.