Taron ministocin kudi na Afrika da shugaban IMF a Zambia
March 16, 2006Shugaban bankin bada lamuni ta IMF Rodrigo Rato na ganawa da ministocin kudi na kasashen Afrika guda shida a birnin Lusakan kasar Zambia,domin tattauna batun yafe basussuzka da inganta gwamnati.Tattaunawar wadda ke gudana a asirce ,na mai zama alamu ne nacewa Zambian ta cimma nasara dangane da darajawa matakan da IMF ta gindaya mata na inganta harkokin tattalin arziki.
Majiya daga Lusakan dai na nuni dacewa ministocin kudi na kasashen Habasha da Ghana da Malawi da Mozambique da Uganda,da kuma mai masaukin baki Zambia ne ke halartan wannan tattaunawa.
Bugu da kari taron na kuma samun halartan wakilan hukumomi masu bada tallafin raya kasashe .
Zambia dai na kasancewa daya daga cikin kasashen Afrika da sukaci gajiyar hukumar bada lamunin ta mdd na yafe basussuka,tsarinda hukumomin bada rance na kasashe suka yafewa,kasashe matalauta da suka dauki matakan inganta tattalin arzikinsu.Tattalin arzikin Zambian dai ya ingantu cikin shekaru 4 da suka gabata.
A jiya ne Shugaban IMF din ya sauka a Lusaka,a rangadinsa na kwanaki 3 a kasar ta Zambia.