Taron ministocin tsaron ƙungiyar EU a Portugal
September 28, 2007Labarai marasa dadin ji ba su karewa daga Afghanistan, inda a ranar laraba aka yi garkuwa da wasu ma´aikata hudu na kungiyar agaji ta Red Cross wadanda ke da alaka da shirin sako wani Bajamushe da ake garkuwa da shi a Afghanistan kimanin watanni biyu da suka wuce. Bugu da kari sojoji biyu na kasar Demark dake aiki karkashin lemar rundunar kasa da kasa ISAF sun rasa rayukansu a kudancin kasar ban da wasu ´yan Spain da suma suka rasu a ranar litinin a yammacin kasar ta Afghanistan. A cikin wannan wata dai sojoji 19 na rundunar ISAF aka kashe a Afghanistan. Minsitan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya bayyana halin da ake ciki a Afghanistan da cewa ya kazanta.
1. O-Ton Jung:
“Tun a bara halin tsaro a Afghanistan ya tabarbare. Hakan kuwa ka na barazanar yaduwa zuwa yankin arewacin kasar. A bayyane yake cewa aikin kiyaye zaman lafiya da sojojinmu na tattare da hadari.”
Daukacin ministocin tsaron dai na shan matsin lamba a kasashensu. A kasar Spain alal misali girke sojojin kasar Afghanistan ya haddasa wata takaddama ta cikin gida yayin a kasar NL kuma ake tabka muhawwara game da amfanin wannan aiki. Yankin da ya fi hadari shine kudancin Afghanistan inda aka girke sojojin Birtaniya da Kanada da NL. To amma yanzu mayakan Taliban sun canza dubarunsu na yaki, inda maimakon fita fili su fafata sun fi kai hare hare na bam da na kwantan bauna.
Yankin dake fama da rikici da nan gaba za´a tura sojojin na kungiyar EU shi ne kasar Chadi. A tsakiyar wannan mako dai kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin tura dakaru wadanda zasu ba da kariya a yankin kan iyakar Chadi da Sudan, inda aka tsugunar da ´yan gudun hijirar Darfur. A lokacin da yake jawabi a gaban babban taron MDD shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya sanya dogon buri.
2. O-Ton Sarkozy:
“Faransa na goyon bayan yi shawarwari bisa manufa. Faransa zata yi haka saboda wanzar da lafiya.”
Ga tawagar da za´a tura Chadi, Sarkozy ya ce zai ba da gudunmawar sojoji dubu daya, to sai dai yanzu haka daukacin su na cikin kasar wadda ta taba zama karkashin mulkin mallakar Faransa. A jimilce tawagar zata kunshi sojoji dubu 4. In ban da kasashen Poland da Sweden wadanda suka yi alkawarin ba da daruruwan sojoji babu wata kasa da ta buga kirjin ba da karo-karon sojoji ba a wani taron neman karo-karon sojoji ga rundunar. A halin da ake ciki majalisar dokokin Turai ta amince da tura da sojojin. A matsayin da ake yanzu sojoji dubu 1 da 500 kadai aka hada kan su wadanda zasu ba da kariya ga sansanonin ´yan gudun hijirar dake yankin kan iyakar Chadi da Sudan mai tsawon kilomita dubu da 300.