Taron minstocin harakokin wajen Russie da China a game da rikicin Iran
May 16, 2006Talla
Ministocin harakokin waje na ƙasashen Rasha, da China sun shirya zaman taro, yau a birnin Mosko.
Li Zhaoxing, da takwararan sa, Sergueei Lavrov, sun tantana a game da rikicin makamman nukleyar Iran.
Ƙasashen 2, sun ƙara jaddada matsayin su, na ƙin amincewa da mattakan da Amurika, da ƙungiyar gamaya turai, ke buƙatar ɗauka a kan Iran.
A wani taron manema labarai, da ministocin 2, su ka kira, sun ce Rasha da China, ko shaka babu, za su hawa kujera naƙi, idan komitin sulhu na Majalisar Dinkin dunia, ya buƙaci kaɗa ƙuri´a, domin ɗaukar matakan soja, a kan Iran.