110610 Klima UN Verhandlungen Bonn
June 12, 2010Wannan tattaunawar dai shi ne irinsa na farko tun bayan taron ƙoli kan yanayi da ya gudana a birnin Kopenhagen a cikin watan Disamban bara. To sai dai sakamakon taron ya nunar a fili cewa rashin nasarar taron ƙolin birnin Kopenhagen na ci-gaba da yin tasiri.
A lokacin da yake magana a taron manema labarai a ƙarshen taron na makonni biyu a nan Bonn, shugaban sakatariyar yaƙi da sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya mai barin gado Yvo de Boer cewa yayi:
"Ina farin cikin sanar da ku a wannan taron manema labarai na ƙarshe da zan yi, cewa mun samu ci-gaba mai ma'ana a wannan babban taron. Dukkan ƙasashen sun tattauna da juna tsakani da Allah. Wannan kuwa shaida ce cewar taron na MƊD ka iya haɗa kan ƙasashe domin yin tattaunawa mai ma'ana idan da niyar yin haka."
Sake maido da yarda shi ne babban aikin wannan zagayen tattaunawar farkon a Bonn bayan na birnin Kopenhagen a watan Disamban bara da aka tashi baram-baram. A tsawon makonni biyu na shawarwarin, mahalarta taron sun yi ta taruka ba dare ba rana. Ko shakka babu fatan da duniya ta yi na samun wani tudun dafawa gabanin taron Kopenhagen ya dusashe, musamman ganin cewa bayan rugujewar taron na Kopenhagen, ya fito fili cewa ba za a iya warware matsalar sauyin yanayi a bugu ɗaya ba. Samun mafita daga wannan matsala abu ne da zai ɗauki lokaci mai tsawo.
"Haƙiƙa alƙawuran da ƙasashe masu arzikin masana'antu suka yi na rage fid da gurɓataccen hayaƙi, har yanzu bai kai yawan da masana kimiyya suka gabatar ba wato ƙasa da kashi 25 ko 40 cikin 100, idan muna son mu samu damar rage ɗumamar doron ƙasa da maki biyu na ma'aunin Celsius. Ko da za mu haɗa dukkan alƙawuran da ƙasashe suka yi ba za mu iya rage yawan ɗumamar yanayi nan da shekaru 10 masu zuwa ba."
To amma duk da haka shugaban na sakatariyar yaƙi da sauyin yanayi na MƊD Yvo de Boer ya ce taron Kopenhagen ya nunar cewa shugabanni na da fatan cimma burin rage maki biyu na zafin yanayin. To sai dai ana rashin wani ƙwaƙƙwaran tsari dangane da yarjejeniyar yanayi ta ƙasa da ƙasa wadda za a tattauna kai a lokacin taron muhalli da zai gudana a birnin Cancun na ƙasar Mexiko a watan Disamba mai zuwa.
Jan Kowalzig masanin yanayi na ƙungiyar Oxfam a Jamus ya ce ba taron yanayi kaɗai ake buƙata domin samun kusantar juna ba, a' a kamata yayi a tarukan ƙungiyoyi kamar G8 da G20 a mayar da hankali kan wannan batu.
"Waɗannan dai wasu ayyuka ne dake tafiya kafaɗa da kafaɗa domin samun wani ƙwarjini a siyasance. Idan hakan bai samu ba, to taron makonni biyu da ma wanda za a yi a birnin Cancun ba za su taimaka a cimma burin da aka sa gaba ba."
A Cancun dai za a yi ƙoƙarin fayyacewa kan sharuɗɗan fid da hayaƙi ga ƙasashe masu tasowa da irin bayanai da kuma taimakon da ake buƙata. Tarukan sharen fage na gaba za a yi su ne a nan Bonn a cikin watan Agusta, sai a China a cikin watan Oktoba.
Mawallafa: Helle Jeppesen / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi