Taron nazarin dumamar yanayi a Bonn
May 8, 2007Sama da kwararru masana kan harkokin yanayi 2000,suka hallara anan birnin Bonn,domin nazarin halinda duniya take ciki na karuwar dumamamar yanayi gabannin babban taron mdd dazai gudana a watan Disamba a Tsibirin Bali.
Taron wanda aka bude daga ranar 7 zuwa 18 ga wannan wata na mayu da muke ciki zaiyi nazarin matsalolin da kasashen duniya ke ciki gabannin babban taro na mdd ,bisa laakari da yadda majalisar tasa fifiko kan wannan matsala ta karuwar dumamar yanayi da kuma hanyoyi da zaa bi na shawo kan matsalar.
Bugu da kari dole ne a samar da kudade da zaayi amfani dasu akan hanyoyi na fasaha da zaa bi na kalubalantar matsalar baki daya,musamman bisa laakari da taron da akayi na yanayi a birnin Nairobin kasar kenya a shekara ta 2006 data gabata domin rage illolin da dumamar yanayin zai haifar.
Babban sakaren gudanarwa na hukumar mdd dake kula da harkokin sauyin yanayi Yvo de Boer ya jaddada muhimmancin mayar da hankali kan wannan matsala..
“Wannan bangare ne dake samun karuwan kulawa.A wani bangare saboda karuwan illoli dake dake tattare da sauyin yanayi,kana a hannu guda kuma bisa sanin cewa kasashe da dama zasu tsunduma cikin matsaloli sakamakon karuwar dumamar yanayi koda a halin yanzu mun fara daukan matakai.Kuma abun takaici shine kasashe matalauta sune wannan matsala zata fi addaba”.
Kasashen nahiyar Afrika dai sune wadannan matsaloli zasu fi addaba, kasancewa mafi yawa daga wasu yankunan wannan nahiya na fama da matsaloli na rashin ruwan sama,kana ga matsaloli na kasarncin ruwan sha mai tsabta.
A yanzu haka dai zaa kashe kimanin dala million 400 na Amurka cikin shekaru 5 masu gabatowa,domin tallafawa wadannan kasashe wajen samun daman cigaba da rayuwa da sauyin yanayi da ake fuskanta.
Matsaloli da zaa fuskanta inji kwararru shine irin fasaha da zaa iya amfani dasu a kasashe masu tasowa,da kuma yadda zaa kalubalanci wannan yanayi bisa laakari da irin matsaloli na rayuwa da kasahen ke fama dasu inji jamiin na mdd Yvo de Boer
“Zaa kirkiro wasu hanyoyi na daban wanda zaa samarwa kasashe masu tasowa kayayyakin aiki da kudade doimin maganta matsaloli ba tare da an rantawa mutane kudade bane?ko kuma matakai zamu zamu dauka nan gaba wanda zai samarda irin tallafi da ake bukata ,wanda zai basu daman samarda karin kudade wanda kuma hakan ne zai magance matsalar sare sare jeji da ake fama dayi.”
Abunda keda muhimmanci anan dai shine kasancewar wannan taro wuri ne na mahawara,shin zaa mayar da hankali kan kasashe matalautan da yadda zaa taimaka musu a zahiri,ko kuma zaa cigaba da zanawa ne akan takarda...
“Yvo de Boer yace ina kyautata zaton zaayi mahawara mai maana a wannan taro ,musamman a yayinda wakilai zasu samu lokaci sosai domin bayyana mana abunda kimiyya ke nunanrwa a halin yanzu”.