1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arziki tsakanin Jamus da Afirka

Gazali Abdou Tasawa AH
October 30, 2018

Taron karfafa saka jari a Afirka na Compact With Africa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shirya a birnin Berlin, ya jaddada bukatar saka jari a kasashen nahiyar.

https://p.dw.com/p/37Obf
Compact with Africa - Teilnehmer beim Bundespräsidenten
Shugabannin kasahen Afirka tare da shugaban Kasar Jamus a tsakiya Frank Walter SteinmeierHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

A jawabin da ta gabatar a wajen wannan taron zuba jari a Afirka na Compact with Africa, Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga masu zuba jari na manyan kasashen duniya da su mayar da hankalinsu a halin yanzu ga nahiyar Afirka a maimakon raja'a da suka yi shekaru da dama kusan kocokam kan nahiyar Asiya domin kuwa a cewarta makomar arzikin duniya na a nahiyar Afirka. Merkel ta kara da cewar idan dai har kasashen Turai na son shawo kan matsala ta kwararar matasan Afirka zuwa Turai, to kuwa ya zamo dole ga kasashen Turai da su dage wajen ganin tattalin arzikin kasashen nahiyar ya bunkasa ta yadda matasa za su samu ayyukan yi. A kan haka ne ma ta ce gwamnatinta ta dauki sabbin matakai na karfafa wannan shiri na zuba jari a AfirkaTa ce: '' Gwamnatita ta gudanar da nazari na kirkiro da sabbin matakai inda muka tsaida shawarar kafa wata gidauniyar kudi ta musamman da za ta taimaka wa kanana da matsakaitan masana'antu a Turai da Afirka ta hanyar ba su basussuka domin samun damar bunkasa harakokin kasuwanci a kasashen Afirka:"

Zuba jari ga kasashen Afirka zai taimaka wajen yaki da ci rani

Deutschland Afrika-Gipfel bei Bundeskanzlerin Angela Merkel
Shugaban Ruwanda Paul Kagame da Angela Merkel da Cyril Ramaphosa na Afirka ta KuduHoto: Reuters/A. Schmidt

Kasashen Afirka 12 ne dai suka aiko da wakillan a taron na birnin Berlin wanda ya samu halartar wasu shugabannin kasashen nahiyar ta Afirka da suka hada da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar da Beji Caid Essebsi na Tunusiya da da Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da Paul Kagame na Ruwanda. A karkashin shirin na Compact with Africa tun a loakcin kaddamar da shi a shekarar da ta gabata shugabannin Afirka sun sha alwashin gudanar da sauye-sauye da kuma kwaskware dokokin zuba jari na kasashensu domin bai wa kasashen duniya kwarin gwiwar zuwa zuba jari a kasashen nasu. Kuma da yake jawabi a wajen wannan taro Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya bayyana wasu daga cikin matakan da nahiyar Afirkar ta dauka. 

Kasashen Afirka na kokarin kara bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar tallafin

Deutschland "Compact with Africa"-Konferenz in Berlin
Shugaban Kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi tare da Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Ya ce: '' Gyare-gyaren da ta yi a fannin harakokin kudi da na dokoki, Kungiyar Tarayyar Afirka ta tsaida samar da kaso 12 daga cikin dari na kasafin kudadenta na shekara mai kamawa domin tallafa wa shirin, kuma kasashen nahiyar ne za su zuba kaso mafi rinjaye na wannan kudin. Kazalika mun saka hannu kan wasu yarjeniyoyin kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashen nahiyar da kuma wasu na kasa da kasa ta yadda Afirka ta zamo tamkar kasa daya a cikin huldar kasuwancin."

Yanzu haka dai tuni wasu kasashen nahiyar ta Afirka suka fara cin moriyar wannan shiri na Compact with Africa inda kasashen Ghana da Tunusiya da Cote d'Ivoire suka samu tallafin kudi miliyan 365 na Euro. Sai dai wasu na ganin rashin shigar kasashe kamar su Najeriya da Kenya a cikin shirin na rage armashinsa. A bin jira a gani dai a nan gaba shi ne tasirin da shirin na Compact with Africa za ya yi wajen samar da ayyukan yi da rage radadin talaucin da ya yi wa mafi yawancin al'ummomin kasashen nahiyar katutu.