Taron sasanta rikicin nukiliyar Iran
May 9, 2006Talla
Ministocin harkokin waje na manyan ƙasashe shida masu faɗa a ji sun gudanar da taro da nufin ɗaukar matsayi guda a game da dambarwar shirin nukiliyar ƙasar Iran. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice, ta ta karbi baƙncin taron na takwarorin ta daga kasashen Rasha da China da Faransa da Britaniya da kuma Jamus a birnin New York. Amurka na kara yin matsin lamba domin ganin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya ɗauki tsauraran matakai a ƙarƙashin sashi na bakwai na ƙudirin majalisar domin tilastawa Iran dakatar da bunƙasa sinadarin Uranium. A waje guda dai rahotanni sun baiyana cewa taron na ministocin harkokin wajen ya tashi ba tare da cimma wani ƙudiri ba.