1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sauyin yanayi na Sahel a Nijar

Zulaiha Abubakar
February 21, 2019

Shugabannin kasashen 17 na yankin Sahel a Afirka za su gudanar da taro a ranar Litinin mai zuwa a Jamhuriyar Nijar don bunkasa shirin sauyin yanayi wanda zai lashe kudaden da ya kai dala biliyan 400 .

https://p.dw.com/p/3Dleu
Eco Africa DW
Hoto: DW

Ministan Muhalli na Jamhuriyar Nijar Almoustapha Garba ya shaida wa manema labarai a birnin Niamey cewar tuni aka ware shekara ta 2018 wacce ta gabata zuwa 2030 a matsayin wa'adin gudanar da wannan aiki na sauyin yanayi. Za kuma a yi amfani da kudaden ne a ayyukan da suka hada da rage amfani da hayaki mai cutar da muhalli da kuma wayar da kan al'umma kan sauyin yanayi, kamar yadda yake cikin yarjejeniyar da kasashe suka rattaba hannu yayin taron sauyin yanayin da ya gudana a shekara ta 2015 a birnin Paris.