Taron shawarta shirin nukiliyar Iran
December 6, 2010Talla
Nan gaba kaɗan idan an jima wakilan ƙasashe shidda da ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya z asu gana a birnin Geneva na ƙasar Sitzerland da nufin tattauna batun shirin Nukliyar Iran, wanda aka dakatar da shi kusan watannin 14. Wannan taro ga alama zai gudana ne cikin wani hali na ƙara tsantsanta, bayan da ƙasar ta Iran ta ce ta ƙara samar da wasu sinadirai na ƙarfen Uranium da ta kan iya sarrafawa. Ƙasashen yamancin duniya na zargin ƙasar da yunƙurin ƙera makaman nukliya da sinadarin-abin da Iran ɗin ta musunta ta kuma ce ta na sarrafa shi ne domin bunƙasa tattalin arziƙinta da rayuwar al'umarta.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas