1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanni uku game da kuɗin Euro

August 5, 2011

Shugabannin ƙasashen Faransa da Jamus da Spain za su yi taro a yau game da rikicin basukan ƙasashen Spain da Italiya da kuma duba matsalar da kuɗin Euro ke fiskanta

https://p.dw.com/p/12Bbu
Shugabannin Turai ciki har da Merkel da Sarkozy da ZapateroHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa da kuma firaministan Spain Jose Louis Rodriguez Zapatero , sun amince su gudanar da wani taron na haɗin guywa a wannan juma'a, da zummar gano bakin zaren warware matsalar bashi da wasu ƙasashen Turai ke fama da ita, wanda ke neman jefa takardar kuɗin Euro cikin wani mawuyacin hali. Fadar mulki ta Paris ɗin Faransa ce ta bayar da wannan sanarwa ba tare da wani ƙarin haske ba, bayan da darajar euro ta karye a kasuwannin hada-hadar hannayen jari na duniya a ranar alhamis.

Dama dai Sakataren zartaswa na ƙungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya tattauna da wasu shugabannin ƙasashen turai game da matakan da ya kamata a ɗauka domin fitar da ƙasashen spain da Italiya daga koma bayan arziki da suke neman faɗawa. cikin wata wasika da ya aikawa shugabannin ƙasashen da ke amfani da Euro, Barroso ya yi kira a garesu da su ƙara yawan kuɗin asusun tallafa wa ƙasashe da ke fama da rikicin kuɗi i zuwa Euro miliyon dubu dari huɗu da 40.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman