1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arziki tsakanin Japan da Afirka

Mahmud Yaya Azare
August 29, 2022

Shugabannin kasashen Afrika da wakilan kasar Japan sun gudanar da taro karo na takwas a kasar Tunisiya don duba hanyoyin bunkasar tattalin arziki da kuma rage tasirin Chaina a nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/4GC3l
Tunesien, Tunis | Japan - Afrika Gipfel
Hoto: Fethi Belaid/POOL/AFP/Getty Images

Fira ministan Japan Fumio Kishida wanda ya isar da sakonsa a taron ta hanyar yanar gizo sakamakon  gwajin da aka yi masa dake nuna cewa yana dauke da cutar Covid -19, ya sanar da bawa Nahiyar ta Afirka tallafin dala miliyan dari, don taimaka mata farfadowa daga annobar corona da kuma tasirin da yakin Rasha da Ukraine suka yi wa tattalin arzikin nahiyar.

Ya ce Japan za ta zuba jarin dala biliyan 30 cikin tsukin shekaru uku a Afirka don bunkasa tattalin arzikinta. Zamu kashe wadannan kudadan ne wajen samar da makamashi mai tsafta da bunkasa cimaka da masana'antu. Za kuma mu yi raba daidai wajen zuba jarin tsakanin masana'antun gwamnati da masu zaman kansu.

Wannan alkawarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Chaina ke kara tabbatar da tasirinta a nahiyar da shirinta na “Belt and Road”, da kuma yadda masana ke nuna damuwa kan mummunan tasirin da rance mai dogon zango da Chaina ke ba wa wasu  kasashen Afirka suke daukarsa a matsayin ingiza mai kantu ruwa da nufin mamaye albarkatun da kasashen ke da su.

Tunesien, Tunis | Japan - Afrika Gipfel
Wakilai a taron Japan da Afirka a kasar TunisiyaHoto: Fethi Belaid/POOL/AFP/Getty Images

Shugaban bankin bunkasa tattalin arzikin Afirka, Dr. Akinwumi Adesina, ya ce akwai bukatar bangarorin biyu su sake matsa kaimi wajen bunkasa alakar da ke tsakaninsu a bangarori mabambanta, idan aka yi la'akari da yadda wannan alakar tsakanin nahiyar Afirka da kasar China ta yi nisa:

Ya ce Japan tsohuwar abokiyar kawancen Afirka ce kuma tun kusan shekaru bakwai da suka gabata alakar cudeni in cudeka tsakaninta da Afirka ta taka gagarimar rawa wajen bunkasa wasu bangarorin tattalin arziki a tsakaninsu sai dai har yanzu akwai bukatar kara azama don bunkasa su.

A nasa bangaren, shugaban Tunisiya Kais Saeed, da ke karbar bakuncin taron wanda kuma kasarsa ke fama da matsalolin siyasar da tushensu gazawar tattalin arziki ne, ya yaba da tallafin na Japan yana mai fatan hakan zai taimaka wajen rage talauci a nahiyar.

Bugu da kari,shugaban na Tunusiya  da ya yaba wa Japan dangane da kiran da ta yi na a gyara zaluncin da aka jima ana yi wa nahiyar Afirka na hana ta kujerar dun dun dun a kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya. Ya sha alwashin hada karfi da karfe da sauran shugabannin Afirka don ganin wannan burin nasu ya tabbata:

Afrika ECOWAS Gipfel
Shugaban kasar Senegal kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka Macky SallHoto: FRANCIS KOKOROKO/REUTERS

Ba makawa mun yi karatun ta natsu a wannan haduwar mai cike da tarihi kan yadda za mu hada karfi da karfe don matsin lambar ganin an bawa nahiyar Afirka wannan kujerar ta din din din, lamarin da ke zama babban buri ga shugabanninmu da suka jagoranci yanta kasashenmu daga mulkin mallaka.

Sai dai matakin shugaban Tunisiya na shirya gagarumar tarba ta kasaita ga shugaban yan awaren Polisario da ke neman ballewa daga Morocco ya tunzura kasar ta Morocco wacce ta kaurace wa taron, lamarin da shugaban Tarayyar Afirka kuma Shugaban kasar Senigal Macky Sal ya siffanta da wani abun takaici:

Senegal ta ji takaicin rashin halartar da Morocco a wannan taron saboda sabanin da aka samu wajen gayyatar wasu a taron, kasancewarta jigo wajen kafa wannan kawancen na kasashen Afirka da Japan muna fata za a magance wannan matsalar baki daya don kauce wa aukuwar irin wannan tangarda a kungiyarmu