Taron tunawa da Ashura ya kare lami lafiya a Iraq
February 9, 2006An kammala bukukuwan Ashura a garin Kerbala na kasar Iraqi ba tare da fuskantar asarar rayuka ko tashe tashen hankula ba.
An dai kiyasta cewa mutane kusan miliyan biyu ne suka halarci bukukuwan na Ashura a garin na Kerbala, wanda ake gudanarwa a ranar 10 ga watan muharram na kowace shekara, don tunawa da rasuwar jikan manzon Allah wato Imam Hussain.
Bayanai daga garin sun nunar da cewa, mabiya darikar ta shi´a sun gudanar da bukukuwan ta hanyar yin maci akan titunan garin dauke da tutoci masu launi iri daban daban, a hannu daya kuma da kulake da kuma adduna da suka bugun kann su dasu.
Kafin dai fara gudanar da wadannan bukukuwa na wuni uku, jami´an tsaro sama da dubu takwas ne suke sintiri don kare kai hare haren kunar bakin wake da kuma dangogin su.