Taron tunawa da harin Charlie Hebdo
January 5, 2016Shugaban Faransa Francois Hollande ya kaddamar da taron tunawa da mutanen da suka rasu a cikin harin ta'addancin da aka kai a cibiyar jaridar Charlie Hebdo da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a ranar bakwai ga watan Janerun shekara ta 2015.
Hollande ya jagorancin taron inda ya kuma kaddamar da wasu alluna guda uku masu dauke da jerin sunayen mutanen da suka mutu a cikin harin. Allunan da aka kafa a gurin da aka kashe 'yan jaridar da kuma a titin da daya daga cikin maharan ya hallaka wani dan sanda mai suna Ahmed Merabet da kuma a kusa da babban shagon Casher na gabashin birnin Paris inda wani shima mai tsananin kishin addinin mai suna Amedy Coulibaly ya hallaka wasu Yahudawa uku da suka je cefane a kantin na Cacher a ranar tara ga watan Janerun shekarar ta 2015.
A ranar Lahadi mai zuwa ce Faransar za ta gudanar da gagarumin taron nuna alhini ga mutanen 17 da suka rasu a cikin harin na Charlie Hebdo dama wasu mutanen 130 da suka mutu a cikin harin birnin Paris na ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata.