1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wadanda hare haren taaddanci ya ritsa dasu a Spain

Zainab A MohammedFebruary 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvS3
Matsalar yan taadda
Matsalar yan taaddaHoto: AP

An kamala taron kasa da kasa a dangane da wadanda matsalar ayyukan taaddanci ta ritsa dasu a kasar Spain.

Taron na kasar Spain dai ya samu halartan wakilai sama da 600 wadannan wadanda matsalar taaddanci ya ritsa dasu ta hanyoyi daban daban,inda dukkanninsu suka amince da shiga dukkan harkoki na yaki da ayyukan taaddanci na kasa da kasa.

Wannan daidato da aka cimma dai na nufin bawa wadannan mutane daman a taka rawa kai tsaye cikin dukkan shirye shiryen yaki da ayyukan taadanci .

Bugu da kari sakamakon taron ya bukaci kafa komitoci zaunananu a mdd da kungiyar gamayyar turai ,wadanda zasu hadar da wadanda matsalar taaddanci ya ritsa dasu.

Comissinan sharia na kungiyar gamayyar turai Franco Frattini,yace ya bada goyon bayansa na kafa kungiyar wadanda wannan matsala ta ritsa dasu ,wadanda kuma a hannu guda zasuyi aiki da masu tsarin shirye shiryen yaki da ayyukan taddanci na kungiyar ta EU.

Frattini…

A nawa raayin akwai bukatar mu dauki matakai na da suka cancanta akan wadanda ke cikin wahala sakamakon hare haren taaddanci.Wannan zai kasace babbar nasara a harkokinmu na gudanarwa,idan sukayi aiki tare damu.

Abunda wannan taro na yini biyu ya mayar da hankali akai dai shine nuna alhini da tausayawa adangane da irin gabatarwar wadannan mutane adangane da halin da suke ciki sakamakon harin daya ritsa dasu.Wasu daga cikinsu dake da zama a garin Valencia dake Spain dai sun samu tallafi da kwarin gwiwa.

Daga cikinsu kuwa akwai wadanda suka tsira da rayukansu daga harin jirgin kasan na na Madrid,da wasu da hare haren kungiyar ETa ya ritsa dasu ,kana akwai wasu daga kasashen ketareda suka hadar da rasha da Amurka.Bugu da kari akwai wadanda suka tsira da rayukansu daga rikice rikicen izraela da palasdinu dana arewacin Irelanda da wasu daga Colombia.

Duk da banbancin tushe da kasa,mahalarta taron sun bayyana takaicinsu a dangane da gazawar mdd wajen fassara maanar kalmar taaddanci.

Akan hakane suka bayyana manufofinsu na yin Allah wadan kowane irin kisan gilla wa fararen hula babu gaira babu dalili.

Jaime Lozada mai shekaru 21 da haihuwa na daya daga cikin wadanda suka tsere daga fadan yan yakin sunkuru a Colombiya,kuma daya daga mahalarta wannan taro.

Lozada..

An sace ni tare da mahaifiyata da kanina.Na zama na tsawon shekaru 3 acikin kungurumin jeji,wanda ya zame mana kamar mutuwace a sannu sannu.Aka sake sace mahaifiyata ,wadda ya ztuwa yanzu tsawon shekaru hudu kena babu labarinta,ko menene ya faru da ita.Ayayinda a watannani biyu da suka gabata ne aka kashe mahaifimmu.

A wannan muhimmin taro na yini biyu da an samu sabanin raayi a dangane da yadda duniya zata kalubalanci matsaslar taaddanci,amma bu mafi muhimmanci shine a sanya wadanda wannan matasala ta ritsa dasu cikin dukkan shirye shirye.