1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron 'yan jaridu da 'yancin fadar albarkacin baki

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 13, 2016

A wannan Litinin din ne aka bude taron shekara-shekara na 'yan jaridu na duniya da tashar DW ta saba gudanarwa a birnin Bonn na Tarayyar Jamus.

https://p.dw.com/p/1J5hd
Taron 'yan jaridu na duniya a Bonn
Taron 'yan jaridu na duniya a BonnHoto: DW/K. Danetzki

A yayin bude taron dai an bayar da kyauta ta 'yancin fadar albarkacin baki ga babban editan jaridar "Hürriyet", ta Turkiyya Sedat Ergin. Jaridar ta "Hürriyet" dai na daya daga manyan gidajen jaridu masu zaman kansu a Turkiyya, a cewar editan jaridar "Bild" ta Jamus Kai Diekmann. Diekmann ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da mukala yayin bude taron na bana na "Global Media Forum". Taron wanda ke samun halartar akalla mutane 2,000 daga akalla kasashe 100 daga sassa daban-daban na duniya, za a shafe tsawon kwanaki uku ana gudanar da shi wato daga ranar 13 ga wannan wata na Yuni zuwa 15 ga wata. Taken taron na bana dai shi ne: "Kafafen sadarwa, 'Yanci, Kyawawan Dabi'u", kuma za a tattauna batutuwa da dama ciki kuwa har da na kare 'yancin dan Adam da kuma rawar da kafafen yada labarai ka iya takawa wajen yaki da cin zarafin mata da kananan yara.