1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙungiyar OPEC a Nigeria

December 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuY0

Ministocin ƙasashe masu arzikin mai na duniya OPEC na gudanar da taro a Nigeria domin yanke shawara ko za su rage yawan man da suke hakowa domin daidaita farashin danyen man a kasuwannin duniya. A watan Oktoban da ya gabata ƙasashen ƙungiyar ta OPEC a taron su da ya gudana a ƙasar Qatar, sun rage yawan da kimanin ganga miliyan daya da rabi a kowace rana, wanda ya sanya adadin man da ƙasashen ke hakowa ya zuwa ganga miliyan 26 da dubu ɗari uku a kowace rana.