Taron neman magance matsalolin tsaro
December 14, 2022Wadanan taruka na Forum ko mahawara da hukumomin jihar Maradi suka shirya a karamar hukumar Gabi da Gidan Sori sun hada wakilan bangarorin al'uma daban-daban da suka hada da sarakunan gargajiya, masu garuruwa,'yan sanda, 'yan majalisa, magajinan gari, kungiyoyin fararen fula da sauran masu ruwa da tsaki kan maganar tsaro na yankin gundumomi Madarounfa da Gidan Roumji. An kuma duba matsalolin tsaro a iyaka da Najeriya ta bangaren jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto.
An dai shirya taruka da zumar samo sabbin shawarwari da dubaru na kawo karshen 'yan ta'adda da 'yan bindiga dadi masu garkuwa da mutane da satar dabbobin da ya zama ruwan dare a wannan yanki. Matsalar dai ta shafi kowa a cewar Gwamnan jahar Maradi Shaibu Abubakar.
Tarukan forum na zuwa lokacin da hare haren da garkuwa da mutane ke dada zafafa tare da jefa alumomin yankunan cikin mawuyacin halin. Abu Mahaman wakilin hukumar karfafa zaman lafiya ta kasa HACP ya bayyana matsayi da shawara hukumar kan matsalar tare da neman smaun taimakon duk bangarorin da suka dace.
Taron ya kuma ya tsaida muhimman shawarwaru da dubaru na bai daya da ke zaton idan an yi anfani da su cikin hikima to babu shakka matasalar za ta kau ko ta yi sauki.