1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarwatsewar bam a ƙasar Girka

March 29, 2012

'Yan sanda a Girka sun cafke mutum guda bisa zargin sa da hannu wajen fashewar bam a wani caji-ofis dake birnin Athens.

https://p.dw.com/p/14UEU
Greek Prime Minister Lucas Papademos addresses the nation during a televised speech in Athens February 11, 2012. Papademos told Greeks they face a collapse in living standards and shortages of fuel and medicine if lawmakers on Sunday reject a multi-billion euro bailout deal and the country defaults on its debt. Papademos spoke on Saturday in a televised address to the nation before parliament votes on a deeply unpopular austerity bill to clinch a 130-billion-euro bailout from the European Union and International Monetary Fund. The words on the bottom read: "A message from Prime Minister L. Papademos." REUTERS/Yannis Behrakis (GREECE - Tags: POLITICS BUSINESS TPX IMAGES OF THE DAY) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS // Eingestellt von wa
Firaministan Girka Lucas PapademosHoto: Reuters

Jami'an 'yan sanda a ƙasar Girka suka ce a wannan Alhamis ce suka tsare wani mutum mai shekaru 29 a duniya bayan wani abu ya tarwatse kusa da wani ofishin 'yan sanda a birnin Athens, fadar gwamnatin ƙasar, wanda kuma ya yi sanadiyyar la'la'ta tagogin ofishin 'yan sanda dama na wasu gine-ginen dake yankin da abin ya faru, amma kuma bai janyo rauni ba ga ko da mutum guda. 'Yan sandan suka ce mutumin da ake zargin, ya harba wani abinda ka iya fashewa ne akan ginin caji-ofis ɗin da misalin ƙarfe biyu da rabi (02:30) na dare agogon ƙasar ta Girka. Wannan caji-ofis dai ya taɓa fuskantar harin bindigogi a shekara ta 2009 daga wata ƙungiyar dake da tsattsauran ra'ayin kawo juyin juya halin siyasa a ƙasar, ko da shike kuma a wancan lokacin babu wanda aka tsare bisa zargin yana da hannu wajen aika-aikar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal