Tashar ruwa ta Cotonou ta daina karbar hajojin Nijar
October 27, 2023Babban daraktan tashar ruwan Cotonou na Jamhuriyar Benin ya ce kasarsa ba za ta ci gaba da karbar hajojin Nijar ba, duk da cewa ita ce mafi kusa da birnin Yamai. Wannan tashar ruwan da ke a nisan kilomita sama 1000 dubu da babban birnin Nijar , amma 'yan kasuwa sun fi amfani da ita wajen shigo da hajoji daga ketare. Tun bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin Mohamed Bazoum ne kasar ta Benin a bisa umurnin kungiyar ECOWAS ta dauki matakin rufe iyakarta da Nijar, lamarin da ya ritsa da tarin hajojin 'yan kasuwan Nijar.
Karin bayanNijar da Benin za su hada karfi a kan makamashii:
A lokacin da yake tsokaci kan wannan mataki, Alhaji Sani chekaraou da ke zama shugaban kungiyar 'yan kasuwar Nijar masu shigo da kaya daga ketare cewa ya yi za su dauki matakan ficewa da hajojinsu daga Jamhuriyar Benin ba tare da ba ta lokaci ba. Shi kwa Alhaji Yacouba Dan Maradi da ke shugabantar kungiyar 'yan kasuwan Nijar ta SEIN cewa lokaci ne ya yi na 'yan kasuwar Nijar su fara tunanin karkatar da akalarsu zuwa wasu tashoshin ruwa. Ita kuwa kungiyar ADDC-wadata mai yaki da tsadar rayuwa a Nijar ta bakin shugabanta Mamane Nouri cewa ta yi akwai bukatar tattaunawa domin bai wa 'yan kasuwa damar karshe ta kwashe kayansu da ke jibge a tashar ruwan Cotonoun zuwa gida.
Karin bayani: Nijar: Shirin yanke huldar tsaro da Benin
Wani rahoton Bankin Duniya ya nunar da cewa tuni tashar ruwa Lome na kasar Togo ta fara cin gajiyar hajojin Nijar da suka fara kaurace wa tashar ruwan Cotonou ta Benin a sakamakon rufe iyakar da ta hada kasashen biyu tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata a kasar Nijar.