1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan arewa na shirin raba Kamaru gida biyu

Salissou Boukari
September 28, 2018

A Kamaru hankali ya karkata ga ranaku biyu da za su kasance na tarihi. Daya ga watan Oktoba 'yan aware na yankin mai magana da Turancin Ingilishi za su kaddamar da 'yanci da bakwai ga wata da ke matsayin ranar zabe.

https://p.dw.com/p/35dvr
Kamerun Buea Wahlplakat Paul Biya
Hoto: DW/H. Fotso

A wannan lokaci da ake yakin neman zabe a kasar Kamaru yayin da kwanaki suka rage a je ga zaben shugaban kasa, idan ka shiga birnin Buea da ke a matsayin babban birnin yankin Kudu maso yammacin kasar, tamkar an yi ruwa an kafe, domin babu wani abu da ke nunin cewa akwai wata cuwa-cuwa ta shirin fuskantar zabe. Birnin mai dauke da ma'aikatu da ma manyan makarantu, ya kasance babu wani babban motsi. Sai dai a mashigar birnin, akwai 'yan sanda da wasu fuskoki a rufe na ayyukan samar da tsaro a wurare dabam-daban da suka girka domin bincike.

Wasu motoci da aka kona jim kadan bayan ka fuce wurin bincike na 'yan sanda, su ne za su tuna maka arangamar da ta wakana tsakanin 'yan aware da jami'an tsaron kasar ta Kamaru 'yan kwanaki da suka gabata. Can gaba kuma bisa babbar hanya kafin ka kai mashiga ta jami'ar birnin na Buea, nan kuma wasu motocin sojoji ne dauke da manyan makamai cikin shirin ko takwana tsaitsaye a daura da hanya. A can gaba kuma tsakanin dakunan kwanan dalibai, da karamar kasuwa ta Molyko, wanda duk shaguna suka kasance a rufe, DW ta yi kitibis da wani Malamin makaranta wanda bai so a bayyana sunansa ba, wanda ya yi tsokaci kan halin da ake ciki:

Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

"Wasu yara na tafiya bisa titi, sai kuma muka ga sojoji na ficewa a guje, can kuma muka ji harbe-hare, nan kawai sai muka ga yara biyu sun fadi kasa a safiyar ranar Litinin din nan da ta gabata, ranar da aka yi yajin aikin kauracewa saye da sayarwa. Kuma ina tsammanin harbin an yi shi ne da gangan, domin idan da harbin ba da gangan ba ne, da sai dai kila wani a same shi ko a kafa ko kuma a ciki, amma dukanninsu biyun an harfe su ne ga kanu."

A halin yanzu jami'ar Katolika ta birnin na Buea ma dai ta kasance a rufe, haka makarantar share fagen shiga jami'a da ke kallon juna da jami'ar ita ma tana rufe. An baza jami'an tsaro a ko'ina, sai dai jama'a na ci gaba da gujewa daga cikin  birnin na Buea yayin da ranar daya ga watan Octoba ke karatowa, ranar da 'yan awaran suka tsayar a matsayin wadda za su kaddamar da incin kan yankin da ake magana da Turancin Ingilishi. Kuma nan gaba da alama birnin na Buea zai kasance sai gidaje da kuma sojoji kaman yadda wannan malamin makaranta yake fargaba:

Vatikan kamerunischer Präsident Paul Biya trifft Papst Franziskus
Hoto: Getty Images/AFP/G. Borgia

"Kamar yanda ku ke gani, birnin tamkar babu kowa a cikinsa. Jama'a sun gudu domin suna tsoron abun da zai wakana. Komai baya tafiya kaman yadda ake so. Lamarin dai ya yi kamari."

Matasa 'yan makaranta da ke cikin wannan birni na Buea na cikin hali na rashin tabbas, kamar yadda za a ji ta bakin wannan matashin dan shekaru 14 da haighuwa wanda ya ce ya yi nadamar yadda lamarin ya kai ga dakatar da karatunsa:

"Muna jin harbe-harbe a wajen da muke. Da zaran wannan tashin hankali ya soma, sai jama'a su soma cece-kuce a kai. Yanzu ya zame mana tilas mu bar wannan wuri ta sabili da matsalar tsaro. bana tsammanin wani abu sai ka kawo mana canji domin samun makoma ta gari a cikin irin wannan yanayi. Ni mutum ne mai sha'awar harkokin sadarwa. Amma yanzu wani abu mai tsananin muni na faruwa."

Kamerun Buea - Unruhen
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

A birnin Muyuka, da Buea da ma sauran garuruwa na yankin, gidaje da dama sun kasance wayam babu kowa a cikinsu. Yankin Kudu maso yammacin kasar Kamaru inda ake magana da Turancin Ingilishi ya kasance babu wani amo na yakin neman zabe a cikinsa kaman yadda yake gudana a yankin da ake magana da Faransanci tun daga ranar 22 ga wannan wata na Satumba da aka soma yakin neman zaben. Sai dai kawai wasu hotunan Shugaba Paul Biya da ake ganin nan da can,  su ne kawai ke nuni da cewa akwai zabe a ranar bakwai ga watan Oktoba mai zuwa.