1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula sun ritsa da Pakistan

December 30, 2012

Jami'an gwamnatin kasar Pakistan sun tabbatar da cewa tsagerun kungiyar Taliban sun hallaka jami'an tsaro 21

https://p.dw.com/p/17BGm
Pakistani army soldiers salute the coffins of their colleagues killed in a gun battle with militants, during a funeral prayer in Peshawar, Pakistan, Friday, Oct. 21, 2011. Militants attacked a group of paramilitary soldiers conducting a search operation in Pakistan's Khyber tribal area Thursday night, sparking fighting that killed three soldiers and 34 militants, said Farooq Khan, a senior government official in the area. (Foto:Mohammad Sajjad/AP/dapd)
Hoto: dapd

Jami'an gwamnatin kasar Pakistan sun tabbatar da cewa tsagerun kungiyar Taliban sun hallaka jami'an tsaro 21, wadanda su ka yi garkawa da su cikin makon da ya gabata.

An yi garkuwar cikin wasu wurare uku na duba ababen hawa da ke garin Peshawar mai fama da tashe tashen hankula. Kuma hukumomi sun tabbatar da haka bayan gano gawauwaki.

Wannan ya nuna yadda har yanzu Taliban ka iya katabus, dukda yadda dakarun gwamnatin kasar ta Pakistan su ka fatattaki tsagerun cikin garuruwan kasar.

A wani labarin gwamnatin kasar ta Pakistan ta ce da sanyin safiyar wannan Lahadi, wani bam ya hallaka mabiya Shiya 17 cikin yankin Kudu maso yammacin kasar.

An kai hari kan 'yan Shiya masu ziyara, a cikin motocin safa. Akwai wasu fiye da 20 da su ka samu raunuka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh