Duniya tana cikin rikice-rikice da ke karuwa
June 28, 2023Wata sabuwar kididdigar zaman lafiya ta duniya, ta gano cewar mace-macen da ake fuskanta a rikice-rikice a duniyar sun zarta na wadanda aka taba gani a baya a wannan karni, inda a bara kadai aka kashe sama da mutane 238,000 a tashe-tashen hankula. Rahoton da cibiyar IEP ta wallafa ya ce duk da yakin da ake yi a Ukraine, bai sanya rikicin kasar ya kasance wanda ya fi zubar da jini ba a duniya.
Karin Bayani: Munich: Macron ya bukaci a karfafa tsaro
Adadin mace-macen da ake samu a tashe-tashen hankula ya kusan ninkawa sau biyu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Hasali ma yake-yaken sun haifar da asarar kashi 13% na bunkasar tattalin arziki na duniya, a cewar kididdigar zaman lafiya ta duniya, wadda cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya (IEP) ta fitar.
Wannan sabon bincike ya bayyana cewa, matsakaicin matakin zaman lafiya a duniya ya ragu cikin shekara ta tara a jere, inda mace-mace suka kai kololuwar da aka cimma a shekarar 2014 a lokacin yakin basasar Siriya. Sai dai karuwar baya-bayannan na da nasaba da yakin da ake yi a Ukraine, inda aka kashe mutane 83,000 a shekarar da ta gabata. Amma dai rikicin da ya fi zubar da jini ya kasance a Habasha, inda mutane 100,000 suka rasa rayukansu.
Sai dai babban abin da ya fi fito fili shi ne rikice-rikice sun zama ruwan dare gama duniya, a cewar Steve Killelea, wanda ya kafa kuma yake shugabantar cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya (IEP), kuma daya daga cikin mawallafin rahoton. Ya ce kasashe 91 na duniya na cikin wani irin rikici, ma'ana an samu karin kasashe 33 idan aka kwatanta da shekarar 2008.
Ana kallon wannan a matsayin wani ci gaba, ganin cewa katsalandan na sojojin kasashen Yamma ta ragu a cikin shekaru goma da suka gabata. Hasali ma dai Amirka da kungiyar tsaro ta NATO sun janye daga Iraki da Afghanistan. Amma, kamar yadda Steve Killelea ya nuna, har yanzu Amirka tana da hannu a cikin rikice-rikice, inda ta kasance babbar mai goyon bayan Ukraine. Wani abu da sabuwar kididdigar ta nuna shi ne yadda ake wuyar samun nasara a yake-yake. Alal misali, an shafe shekaru 9 zuwa 12 ana fama da rikice-rikice a kasashen Yemen da Siriya, kuma babu wata alama da ke nuna cewa za a iya samun nasarar soji a yake-yaken.
Kididdigar zaman lafiyar ta ce kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ke amfani da jirage marasa matuka ya ninka sau biyu tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, kuma adadin hare-haren da jiragen ke kaiwa ya ninka sau uku a lokaci guda. Iceland ta kasance kasa mafi zaman lafiya a duniya, matsayin da take kai tun 2008, yayin da Afghanistan yanzu ta kasance kasa mafi karancin zaman lafiya a duniya a karo na takwas a jere. Hakazalika, Yemen da Siriya da Sudan ta Kudu da da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango suna cikin kasashe 10 mafi karancin zaman lafiya a duniya tun bayan kaddamar da wannan kididdigar a shekara ta 2007.