Tashin bama-bamai a ofishin jakadancin Amirka a Pakistan
April 5, 2010Talla
Aƙalla mutane takwas sun mutu a lokacin wani harin ƙunar bakin wake da aka kai a ƙaramin ofishin jakadancin Amirka da ke Peshawar a arewacin Pakistan. Mayaƙan sa kai waɗanda ke ɗauke da muggan makamai cikin motoci ne suka nufi ginin da ke ƙunshe da masu tsaron ofishin jakadacin. Ɗaya daga cikin mayakan na ɗauke da sama da kilo 100 na bam. Wannan harin ya zo ne sa´o´i ƙalilan bayan wanda ya salwantar da rayukan mutane 38 a lokacin wani taron siyasa na jam'iyyar 'yan kabilar Pashtun. Jam'iyyar ta na bukin nuna farin cikinta game da giramawa kabilar Pashtun da ke zama mafi rinjaye a wannan yanki da hukumomin suka yi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu