Ghana tana kan gaba a tashin farashi
November 9, 2022Kasar Ghana ta samu tashin farashi fiye da kashi 40 cikin 100 a watan Oktoban da ya gabata adadi mafi yawa da kasar ta gani cikin fiye da shekaru 20. Tun farko a watan Satumba an samu tashin farashi na kashi 37 cikin 100, abin da yake nuna yadda darajar kudin kasar ke ci gaba da karyewa idan aka kwatanta da sauran manyan kudade na kasashen duniya.
Kudin kasar ta Ghana da ake kira Cedi ya zama mafi faduwa a duniya a watan Oktoba da ya gabata idan aka kwatanta da kudin Amirka na Dalar a shekara ta 2022 inda kudin ya rasa rabin darajar da yake da ita.
A karshen mako dubban mutane sun fito zanga-zanga a titunan birnin Accra fadar gwamnatin kasar kan neman Shugaba Nana Akufo-Addo ya ajiye aiki saboda tashin katabus bisa tashin farashin abinci da makamashi, inda masu kananan sana'oi ke ci gaba da rufewa sakamakon tsadar rayuwa da tashin farashi fiye da kima.