Tashin hankali sakamakon cutar Ebola
Gwamnatin Laberiya na amfani da 'yan sanda da sojoji wajen daƙile yaɗuwar cutar Ebola. A Monrovia babban birnin ƙasar sun tarwatsa jama'ar da ke yin zanga-zangar ƙin amincewa da matakin gwamnatin.
Kulake da bindigogi
Gwamnatin Laberiya ta ɗauki matakai a kan al'umma, mutane huɗu suka raunata a sakamakon arangamar da aka sha a birnin Monrovia a zanga-zangar da jama'a suka yi waɗanda sojoji suka yi amfani da kulake domin tarwatsa su.
Datse unguwanni
Jama'ar birnin sun ce 'yan sanda sun datse unguwannin da ke da akwai masu fama da ciwon na Ebola da ke a yammancin birnin Monrovia domin hana shige da fici, a wata cibiya inda wasu jama'ar suka kai hari inda aka killace masu ciwon na Ebola domin jinyarsu.
Zanga-zanga da tashin hankali
Zanga-zanga ta ɓarke inda wani jami'in gwamnati da iyalensa lamarin ya so rutsa wa da su, sai da ceton jami'an tsaro waɗanda masu zanga-zangar suka yi musu ruwan duwatsu.
Ƙoƙarin tserewa
'Yan sanda da sojoji sun tinkari masu zanga-zangar da barkono tsohuwa da kulake tare da harba harsassan gaske ga jama'ar da ke ƙoƙarin tserewa daga cibiyar, inda ke da akwai waɗanda ke ɗauke da ƙwayoyin cutar ta Ebola.
An rufe shaguna
Yanzu ƙura ta kwanta a kan tittunan da ke a shiyar yammaci na birnin Monrovia, inda kimanin mutane dubu 75 suke rayuwa a cikin wani yanayi na cinkoso, waɗanda da dama daga cikinsu ba su da ruwan sha. A shiyar da ke kusa da birnin wadda ka iya zama mafi gaggawar yaɗuwar cutar ta Ebola.
Sirleaf ta ce: ''Allah zai ceci ƙasar''
Shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta yanke shawarar ɗaukar matakin killace masu fama da ciwon a cikin yankunan karkara na Dolo da sauransu. Ta kuma kafa dokar hana fitar dare a lokacin wani jawabi da ta yi ta kafofin yaɗa labarai na ƙasar saboda abin da ta kira ceton rayukan jama'a.
Har ya zuwa yanzu babu maganin cutar
Laberiya na ɗaya daga cikin ƙasashen yankin yammacin Afirka da suka fi kamuwa da cutar ta Ebola, inda kusan mutane 600 suka mutu da cutar mai saurin kisa. Ana kamuwa da Ebola ne ta hanyar jini ko yawu, da dai sauransu kuma ba ta da magani.
Tare da taimakon Allah
Ƙungiyar lafiya ta duniya WHO na ƙoƙarin ganin an kawar da cutar cikin watanni masu zuwa, musammun ta hanyar mayar da hankali wajen ƙaddamar da kamfe na wayar da kan al'umma ga yin tsabta. Wannan limamin Cocin a bakin teku a birnin Monrovia na roƙon taimakon Allah domin yaƙi da cutar don kawar da ita.