1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na ci gaba da gigita Zirin Gaza

October 11, 2023

Isra'ila dai ta sha alwashin rikita yankin Falasdinawa da hare-haren ramuwar gayya daidai lokacin da kungiyar Hamas ta ce za ta kashe sojojin Isra'ilan da ta yi garkuwa da su da zarar aka kai mata hari.

https://p.dw.com/p/4XNpS
Hoto: Ohad Zwigenberg/AP/picture alliance

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce kawo safiyar wannan Laraba adadin mutanen kasar da suka mutu a sabon rikicin da ya barke tsakaninsu da kungiyar Hamas ta Falasdinawa mai iko da yankin Zirin Gaza ya kai 1,200. Mai magana da yawun rundunar Jonathan Conricus ya ce wannan adadi abin damuwa ne musamman la'akari da cewa fararen hula ne suka fi yawa a cikin wadanda suka mutun.

Shugaba Joe Biden na Amirka ya jaddada goyon bayansu ga kasar Isra'ila, yana mai gargadin 'yan siyasar da guje wa siyasantar da rikicin.

A Faransa kuma, hukumomi sun kaddamar da bincike kan jam'iyyar NPA mai tsattsauran ra'ayi bayan da ta ayyana goyon bayanta ga Falasdinawa tare da sukar matakan Isra'ila a wannan rikici da ya barke a karshen makon da ya gabata.