1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankalin matasa a London

August 9, 2011

Yau an shiga rana ta uku ta zanga-zangar matasa a birnin London kasar Ingila, inda suke baiyana rashin jin dadin su a game da kisan da suka ce yan sanda sun yi wa wani matashi a birnin a kwanakin baya.

https://p.dw.com/p/12DiR
Tashin hankali da kone-kone a LondonHoto: AP

Yanzu dai kawanaki da dama kenan tun da matasa suka fara mummunan zanga-zanga a London, babban birnin Ingila. Zanga-zangar da aka fara tun ranar Asabar, matasan sun kafa tushen ta ne domin baiyana rashin jin dadin su a sakamakon kisan da suka ce yan sanda sun yi wa wani mataki a birnin a kwanakin baya. Wannan tashin hankali, inda yan sanda suka nuna cewar mutane da dama sun ji rauni, an kuma bata dukiyoyi mai tarin yawa, ta haddasa rikicin siyasa a kasar ta Ingila, inda Pirayim minista David Cameron ya katse hutun ya koma London, kuma ya kira taron gaggawa na majalisar dokoki domin duba wnanan al'amari.

A halin da ake ciki kuma, yan sanda sun sanar da cewar bashi da laifi a game da kisan Mark Duggan, matakin da mutuwar sa ta haddasa tashin hankalin tun daga ranar Asabar da ta wuce. Yan sandan suka ce zasu dauki matakai masu tsanani kan duk wadanda suka ci gaba da kokarin barnatar da dukiyoyin jama'a ko neman haddasa asarar rayukan mutanen da basu ji ba, basu gani ba a yankunan kasar ta Ingila sakamakon zanga-zangar.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala