Tasirin faduwar farashin man fetur
Farashin danyen mai na ci gaba da faduwa sakamakon yawan da ya yi kasuwannin duniya. Lamarin da ya jefa tattalin arzikin wasu kasashe cikin mawuyacin hali.
Farashin fetur ya dagula lissafi
Hatta Norway ba ta tsira daga faduwar farashin man fetur ba. Wannan kasa ta samu bunkasar tattalin arziki a shekarun baya-bayannan sakamakon arzikin man fetur. Sai dai rikidar da ta yi daga matalauciyar kasa zuwa mai bunkasar arziki a duniya bai zi iya dorewa ba, matikar ba ta sanya batun kafa masana'antu da kuma kamun kifi a cikin manufofinta na tattalin arziki ba.
Matsaloli biyu a Rasha
A Rasha, faduwar farashin danyen mai ya zama karaya a kan targade, saboda matsalar ta zo daidai lokacin da tattalin arzikinta ke fama da takunkumin kasashen Turai. A 2015 tattalin arzikin wannan kasa ya ja baya da 4%. Saboda haka aka rage albashin ma'aikata, yayin da darajar kudin Rubel ya ragu da kashi 50%. Cibiyar Bloomberg ta kiyasta cewar a 2016 matsalar tattalin arzikin za ta ci gaba a Rasha.
Rashin tabbas ga makomar fetur
Najeriya ce kasar da ta fi kowacce hako fetur a Afirka. Kafin ya zama shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai kara inganta halin rayuwar talakawa. Amma fadin farashin man fetur ya sa ba zai cika wannan alkawari ba. Bankin Duniya ya nunar da cewar gwamnatin Najeriya na samun kashi 3/4 na kudinta daga man fetur. Akasarin ayyukan raya kasa na jiran gawan shanu.
Halin da farashi ke ciki
Ba Najeriya ce kadai ke dogaro kan man fetur wajen samun kudin shiga ba. Saboda haka ne aka samu gibi tsakanin kudin da ake sa ran samu da kuma farashin da aka sayar da mai a kasuwanni. Farashin ya fadi kasa warwas tun tsakiyar shekara ta 2014. Masana sun nunar da cewar zai dau lokaci kafin farashin ya koma $120 (110.76 Euros) da aka sanshi da shi.
Bayan dage takunkumi kan Iran
Tun bayan da aka dage takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba wa Iran, kasar ta yanke shawarar hako ganga rabin Miliyan na danyen mai a rana - Lamarin da ya sa danyen man fetur ya zama tamkar Jompa a Jos a kasuwannin duniya. Kasar ta Iran ta zargi abokiyar hamayarta Saudiyya da haddasa faduwar farashin man a duniya.
Kaikayi ya koma kan mashekiya
Saudiyya ta ki rage yawan man da take hakowa domin kare kanta daga gasar cinikin da take yi da Amirka da Iran. Amma yanzu kasar da ta fi kowacce hako danyen mai a duniya ta fara girban abin da ta shuka. Asusun Lamuni na Duniya ya gargadeta kan gibin da za a iya samu a kasafin kudi. Kasar na son sanya haraji tare da cire tallafin makamashi da na abinci.
Har yaushe za a ci gaba da dogaro kan mai?
Kamar takwararsu ta Saudiyya, rijiyoyin man fetur na wasu kasashen yankin Gulf irinsu Qatar, Oman da Hadaddiyar Daular Larabawa sun ja baya. Wadannan kasashen da ake ji da su a yankinsu sun jibge kudi a manyan bankunansu - Amma kasashen shida sun rigaya sun samu gibi a kasafin kudinsu na sama $260 billion (239.8 billion Euros), bisa ga kiyasin cibiyar JP Morgan Chase.
Guguwar sauyi ta kada a Banizuwela?
Banizuwela ta fi kowa yawan rijiyoyin mai a duniya, kasar da gwamnatinta ke bin matsakaicin tsarin gurguzu, ta yi amfani da kudin fetur wajen aiwatar da manufofinta na taimaka wa al'umma. Amma shugaba Nicolas Maduro ya kafa dokar ta baci a fannin tattalin arziki. Tun shekarar da ta gabata goyon bayan da magajin Hugo Chavez ke da shi ya ja baya - kamar yadda farashin mai ya yi a kasuwannin duniya.
Ina mafita?
Godiya ta tabbata ga nau'in makamashi da Amirka ke hakowa, wanda ya bata damar zama kasar da ta fi kowacce hako makamashin a duniya. Faduwar farashin fetur ya sa wannan nau'in makamashi ba ya samun karbuwa sosai. Masu ababen hawa na sayan mai da araha, lamarin da ya sa suke sayan motocin kawa da ke zukar mai sosai - lamarin da ke gurbata muhalli.