1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya

October 14, 2010

Shugaban ƙasar Iran Amadinejad yana ziyarar tarihi da ke cike da kace-nace a ƙasar Lebanon, inda ya samu gagarumar tarba.

https://p.dw.com/p/Pdso
Ziyarar Mahmoud Ahmadinejad a LebanonHoto: AP

Shugaban ƙasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad yana ziyarar kwana biyu a ƙasar Lebanon, bayan da a jiya ya ratsa cikin birnin Beirut a tsaye cikin wata buɗaɗɗiyar mota, dubban masu goyon bayan Iran suka fito kan titi suna kaɗa tutar Iran da jinjina wa ƙasar, Ahmadinejad ya kuma gana da Shugaba Sulaiman na ƙasar ta Lebanon, inda suka yi jawabin haɗin-gwiwa ga manema labarai. Duk da hatsari kan tsaro da ake yi masa, Ahmadinejad a yau zai kai ziyara a wani yankin da ke iyakar Lebanon da Isra'ila. A wannan ziyarar dai ana sa ran shugabannin biyu za su sanya hannu kan yarjeniyoyin hulɗar tattalin arzi´ƙi da sauran batutuwan da suka shafi yankin. A yammacin yau ne ake sa ran Ahmadinejad zai gana da jagoran ƙungiyar Hizbollah, Hassan Nasarullah inda ake sa ran ganin Nasurallah a kafaɗar Ahmadinejad yayin wani rali da za su yi a binin Beirut.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas