Tasirin Olusegun Obasanjo a jam'iyar PDP
April 4, 2012A Najeriya murabus ɗin da shugaban kwamitin amintatu na jamiyyar PDP Cif Olusegun Obasanjo ya yi bisa kan wannan mukami bayan daɗewar da aka yi ana ja in ja da ma nuna bugƙatar hakan ya sanya tambayar tasirin da sauakar tasa za ta yi ga jamiyyar da ma dimukurɗiyyar Najeriyar.
To fararre dai kararre ne in ji Hausawa domin kuwa bayan daɗewar da aka yi ana zura ido, kiraye-kiraye da ma amfani da harka da irin ta siyasa tsohon shugaban Najeriyan da ke zama jigo a jamiyyar ta PDP da ke mulkin Najeriyar tun daga 1999 ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kwamitin amintatu na jamiyyar ta PDP.
Tasirin Obasanjo a PDP
Sanin irin tasirin da wannan kwamiti ke da shi a fanin juya akalar inda jamiyyar ta dosa da ma maƙalewar da Cif Obasanjon ya yi a kan wannan muƙami da bisa al'ada ya kamata da daɗewa ya sauka daga kansa ya sanya tambayar tasirin da wannan ka iya yi ga jamiyyar musamman batun dimokɗiyya ta cikin gida ta jamiyyar da yadda mulkin dimukurɗiyyar ke tafiya a Najeriyar. Malam Bukhari Muhammad darakta ne a cibiyar nazarin dimukurɗiyya da ci gaban ƙasa da ke Abuja. Wanda tabbas saukar Obasanjo a muƙamin shugaban amintattu na jam'iyar PDP yana da tasiri.
Rawar da Obasanjo ya taka a PDP
Bisa la'akari da irin rawar da tsohon shugaban Najeriyar Cif Obasanjo ya taka wajen samuwar gwamnatin Najeriya a karkashin shugaba Goodluck Jonathan da ma yadda yake kai ƙwauro yana kai mari a ƙoƙarin jamiyyar na sake kame jihohin kudu maso yammacin Najeriya da jamiyyar adawa ta ACN ta yi masu cin kaca a zaben da aka yi a bara, ya sanya tambayar ko dai Cif Obasanion ya fara rasa tasirinsa ne a jamiyyar ta PDP ya sanya shi ɗaukar wannan mataki, abinda Malam Bashir Baba da ke sharhi a kan al'ammuran Najeriya ya bayyana da cewa akwai alama.
A yayinda za'a ci gaba da sa ido ga irin salon mulkin da sabon shugaban jamiyyar PDP Alhaji Bamanaga Tukur zai yi a jamiyyar ta PDP da ke zama mai tsole idanu ga yadda siyasa ke tafiya a Najeriya, abu muhimmi shine jiran ganin ko Cif Obasanjo ya ja gefe ne ko kuwa akasin hakan ne zai faru.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman