Tasirin rikicin Rasha da Ukraine a wasanni
March 28, 2022Madallah. Bari mu fara da batun neman kai wa ga wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a fafata a Qatar, inda kawo yanzu kasashe 20 cikin 32 da za su fafata a gasar suka samu damar shiga ciki kuwa har da mai masaukin baki Qatar. Sai dai kuma duk cikin kasashen da suka samu damar shiga gasar kawo yanzu babu kasar Afirka ko guda, abin da ke nuni da cewa akwai sauran aiki a gaban kasashen na Afirkan da ke jin kanshi-kanshin samun damar kai wa ga wasan karshen na gasar cin kofin kwallon kafa na duniyar.
A karon farko cikin shekaru 36 kasar Kanada ta samu damar zuwa gasar cin kofin kwallon kafar na duniya da za a fafata a Qatar daga ranar 21 ga watan Nuwambar wannan shekara a kuma kammala a ranar 18 ga watan Disambar bana. Bukuwa da tsallen murna dai ya barke a kasar ta Kanada bayan da ta lallasa Jamaika da ci hudu da nema a Toronto, nasarar kuma da ta ba ta damar shiga gasar ta cin kofin duniya a bana. Tun shekara ta 1986 a gasar da aka fafata a kasar Mexico, rabon da Kanadan ta samu damar shiga gasar. Ita ma dai Amirka ta samu shiga gasar, bayan da ta lallasa Panama da ci biyar da daya. Tun shekara ta 2014 dai, rabon da Amirka ta samu shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniyar. Kasashen da tuni suka samu damar shiga wannan gasar dai, sun hadar da Jamus da Denmark da Brazil da Faransa da Spain da Ingila da Japan da Netherlands da Iran da Saudiyya da Koriya ta Kudu.
Tun bayan barkewar fada tsakanin kasashen Rasha da Ukraine dai, hukumomin kula da al'amuran wasanni daban-daban suka fara mayar da Rashan da 'yan wasanta saniyar ware ta hanyar haramta musu shiga kowanne irin wasa.
Mai rike da kambun tseren motoci wato Formula 1 Max Verstappen ya samu nasara a kan abokin karawarsa Charles Leclerc a daf da kammala gasar tseren motocin da ake fafatawa a kasar Saudiyya. Wannan dai na zaman nasararsa ta farko a kakar wasanni ta bana, kana ta 21 a tsawon shekarun da ya kwashe yana fafatawa a gasar ta Formula 1. Leclerc ya yi fatan lashe gasar bayan da ya samu nasara a yayin bude gasar a Bahrain, sai dai kuma Verstappen bai ba shi wannan dama ba. Shi kuwa fitattcen dan tseren motocin nan da ke tuka mota kirar Marsandi Lewis Hamilton ya kammala a matsayi na 10 bayan da ya fara gasar a matsayi na 15.