Tattauna batun aikin hajji tsakanin Iran da Saudiyya
April 15, 2016Talla
Wannan dai ita ce haduwa ta farko a hakumance tsakanin hukumomin biyu na Saudiyya da Iran tun bayan tsinke huldar diflomasiyyar da suka yi a watan Janairu da ya gabata, bayan da wasu masu adawa da kisan da aka yi wa shehin malamin nan na Shi'a a Saudiya, suka kai hari a ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya a birnin Teheran.
A baya dai Saudiyya ta haramta dukannin wata zirga-zirgan jiragen sama tsakaninta da Iran sakamakon katse huldar diflomasiyyar. Kasashen biyu dai na da mabanbantan ra'ayoyi bisa fannoni da dama, kamar na yaki a kasar Siriya, inda Iran ke tallafawa gwamnatin Bashar Al-Assad yayin da Saudiyya ke taimaka wa 'yan tawaye.