1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: A tattauna yarjejeniyar Iran

Abdourahamane Hassane
November 19, 2018

Ministan harkokin waje na Birtaniya Jerey Hunt zai kai ziyara Iran domin tattaunawa a kan makomar yarjejeniya makamashin nukiliyar Iran da batun yakin Siriya da kuma na Yemen.

https://p.dw.com/p/38U3X
Jeremy Hunt ministan harkokin waje na Birtaniya
Jeremy Hunt ministan harkokin waje na BirtaniyaHoto: picture-alliance/Zumapress/A. Mccaren

Wannan shi ne karo na farko da wani jami'in diplomasiya daga kasashen yammanci duniya zai kai ziyara a Iran, tun bayan da Amirka ta janye daga yarjejeniyar. Shugaba Donald Trump na Amirka ya janje daga yarjejeniyar wacce aka cimma tun a shekara ta 2015, a cikin watan Mayun da ya gabata tare da sake kakaba wa Iran din wani sabon takunkumin karya tattalin arziki, duk kuwa da cewa kasashen duniya sun riga sun cire takunkumin a sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da Iran din.