Tattaunawa a kan batun nukiliyar Iran
October 15, 2014Sake komawa kan teburin tattaunawar dai na daga cikin ƙoƙarin da suke na shawo kan ban-bancin da ke tsakaninsu dangane da batun nukiliyar ƙasar Iran ɗin da ake ta taƙadddama a kai. Ƙasashen da ke da Ƙarfin faƊa a ji a duniya guda biyar da kuma Jamus na da tsahon makwanni shida wato nan da 24 ga watan Nuwamba mai kamawa, su kawo Ƙarshen matsalolin da ke yin tarnaƘi a batun na nukiliya domin daƙile Iran ɗin daga mallakar makaman ƙare dangi da suke zargin Iran ɗin na yi. Tehran dai ta sha musanta wannan zargi, ta na mai cewa shirinta na zaman lafiya ne. Kerry ya shaida wa manema labarai cewa ba zai ce ba za su kai ga shawo kan matsalolin da ke tsakaninsu ba, sai dai kawai akwai gagarumin aiki a gabansu.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane