1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa a kan shirin nukiliyar Iran

October 15, 2013

Birnin Geneva zai sake karbar bakuncin taro a kan nukiliyar Iran a karo na uku.

https://p.dw.com/p/19zWn
A security guard walks near a sculpture of a naked man covered up by a curtain behind the European and Iranian flags on October 14, 2013 at the United Nations' Geneva offices, ahead of fresh talks between world powers and Iran on its controversial nuclear programme. The cover-up of the marble man and his clearly visible penis was first reported by the Swiss newspaper Tribune de Geneve, which claimed that the aim was to avoid offending the Islamic republic's delegation talks. Swiss officials declined to address the newspaper's claim, and told AFP that the aim was to provide a neutral backdrop at the entrance to the meeting hall. AFP PHOTO / FABRICE COFFRINI (Photo credit should read FABRICE COFFRINI/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Manyan kasashen da ke da karfin fada a ji a duniya na dab da shiga wata sabuwar tattaunawa a wata cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva a wannan Talatar (15. 10. 13), domin gudanar da taron yini biyu a kan shirin nukiliyar Iran wanda a ke takaddama a kansa. Wannan kuwa na zuwa ne a dai dai lokacin da masu ruwa da tsaki cikin lamarin, ke kara yin matsin lambar neman cimma maslaha a kan batun, tare da sabuwar gwamnatin Iran mai matsakaicin ra'ayi. Sabon shugaban na Iran, Hassan Rouhani dai, na fatan samun ci gaba a takaddamar, domin bada damar cire wasu daga cikin takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa kasarsa musamman ta fuskar tattalin arziki.

Sai dai kuma ana jajiberin taron ne, dukkan bangarorin biyu, suka ce babu wata alamar samun ci gaba mai ma'ana hatta a wannan jikon. Ministan kula da harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif na daga cikin wadanda za su halarci taron, tare da wakilan kasashen Amirka da Faransa da Rasha da Birtaniya da China da kuma Jamus. Iran dai ta jaddada cewar shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne yayin da kasashen yammacin duniya kuwa ke cewar na samar da makaman nukiliya ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu