1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran ta yi armashi

April 14, 2012

Jakadun yammacin Turai sun ce a wannan karon tattaunawa ta yi armashi a ganawar da suka yi da Iran game da shirinta na nukiliya

https://p.dw.com/p/14e38
Turkey's Foreign Minister Ahmet Davutoglu, left, and Iran's Chief Nuclear Negotiator Saeed Jalili, right, seen with diplomats from the two countries during their meeting in Istanbul, Turkey, Friday, April 13, 2012. After years of failure, Iran and the six world powers may finally make some progress on nuclear negotiations when they meet again Saturday if each side shows willingness to offer concessions the other seeks.(Foto:Burhan Ozbilici/AP/dapd).
Hoto: dapd

Jakadun manyan kasashe shida masu cigaban tattalin arziki na duniya sun gana a yau da jami'an Iran a birnin Istanbul na kasar Turkiya game da shirinta na nukiliya. Wani jakadan tarayyar Turai a tattaunawar wanda ya bukaci a saya sunansa yace a wannan karon tattaunawar ta yi armashi sabanin wadanda suka gabata. Ana kuma fatan gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar a nan gaba. Fiye da shekara guda kenan da tattaunawa ta ci tura tsakanin Iran da kasashen na yammacin turai akan takaddamar nukiliyar Iran. Ganawar da jakadun manyan kasashen shida wadanda suka hada da Amirka da Birtaniya da Faransa da Rasha da China da kuma Jamus suka yi da jami'an Iran na da nufin samo hanyoyin warware takaddamar nukiliyar ta hanyar diplomasiyya. Iran dai ta dage cewa bata da burin kera makamin kare dangi kuma shirin nukiliyarta na lumana ne, sai dai kasashen yammaci suna fargabar bunkasa sinadarin Uranium da Iran ke yi yana iya kaiwa ga kera makamin na Atom a asirce.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh