1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa kan rikicin Ukraine a Berlin

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2016

A karon farko an fara wani taro tsakanin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a Berlin babban birnin kasar Jamus da nufin kawo karshen rikicin Ukraine.

https://p.dw.com/p/2RNnu
Russland Merkel und Putin
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir PutinHoto: imago/ITAR-TASS/M. Metzel

A ranar Laraba 19 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki, Shugaba Putin da kuma shugaban kasar Ukraine din Petro Poroschenko da na Faransa François Hollande za su gana domin tattaunawa kan mafita dangane da rikicin na Ukraine. Shugabannin kasashen uku dai wato Rasha da Ukraine da kuma Faransa kana da shugabar gwamnatin Jamus mai masaukin baki, zasu tattauna domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar birnin Minsk da aka cimma cikin watan Fabarairun shekarar da ta gabata ta 2015, wadda in har aka bita sau da kafa za a iya kawo karshen rikicin na kasar Ukaraine, da ke afkuwa tsakanin gwamnati da 'yan awaren gabashin kasar wadanda ke samun goyon bayan Rasha. Tun bayan barkewar rikicin a shekara ta 2014 kawo yanzu dai, mutane 10.000 ne suka rigamu gidan gaskiya.