1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine kan iskar Gasta fuskanci tsaiko

Muntaqa AhiwaApril 10, 2015

Hukumar kasashen Turai, ta sanar da dage zaman tattaunawa tsakanin kasashen Rasha da Ukraine kan makamashin Iskar Gas wanda aka shirya yi Talatan nan da ke tafe

https://p.dw.com/p/1F6AX
Ukraine Gas Kompresserstation in Chervonodonetsk
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Kozlov

Hukumar ta EU cikin wata sanarwar da ta fitar yau Juma'a, ta ce a yanzu kasashen biyu za su yi taron a mataki na kwararru a birnin Brussels na kasar Belgium a mako an gaba, maimakon tsarin haduwarsu a wannan Talatar.

Zama kan batun makamashin na Gas da kasashen suka shirya dai, an soma shi ranar 20 ga watan jiya, da nufin ceto aikin samar da Iskar daga Rasah ga Ukraine, tun kafin a kai bazara ta gaba.

Wasu majiyoyi daga bangaren Ukraine dai na cewa Rasha ce ta ki halartar tattaunawar da aka tsara za a yi a birnin Berlin na Jamus ranar Litinin, ba tare da ta bayar da wani dalili ba.