Tattaunawar Rasha da Ukraine ta ci tura
April 22, 2022Talla
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya shaidawa taron manema labarai cewa a halin da ake ciki yanzu tattaunawar ta tsaya cik saboda bukatun da suka gabatar wa mashawartan Ukraine kwanaki biyar da suka gabata har yanzu basu bada amsa akansu ba.
Lavrov yace kalaman da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da mashawartansa suke yi a baya bayan nan sun nuna basa bukatar tattaunawar wadda suka dora makomarsu a kai.
A waje guda kuma Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai kai ziyara Moscow a ranar Talata domin ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin.
A kwanakin baya ne dai babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci ganawa da Putin domin tattaunawa kan yakin na Ukraine.