Makomar Siriya a siyasance
December 26, 2015Talla
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan harkokin Siriya Staffan de Mistura ya bayyana fata da ke akwai na shiga tattaunawa da bangarori masu gaba da juna a kasar Siriya, wato bangaren shugaba Bashar al-Assad da bangaren 'yan adawa tun daga ranar 25 ga watan Janairu a Geneva kamar yadda ofishin jakadan ya bayyana a ranar Asabar din nan.
A cewar jawabin da ke fitowa daga ofishin na De Mistura ana kara azama kan duk wasu matakai da za su kai ga wannan tattaunawa a wannan rana da aka tsara tare da neman hadin kan dukkanin bangarorin, sannan jawabin ya kara da cewa ba za a yi sakaci ba shirin da aka fara samun ci gaba a kansa na tattaunawar sulhu ya fiskanci wata matsala.