Tauraron wasan ƙwallon Afirka
March 12, 2010Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Afirka ta zaɓi kepten ɗin Kot-divuwar a matsayin gwani na gwanayen ƙwallo na nahiyarmu na bara. A lokacin wani ƙasaitaccen biki da ya gudana a birnin Accra na ƙasar Ghana, waɗanda suka kaɗa ma Didier Drogba ƙuri´a sun nunar da cewa rawar da ya taka wajen shigar da ƙasarsa cikin jerin ƙasashen Afirka a wasannin kofin duniya ne ya sa suka karramashi. Ƙwallaye tara ne dai Didier Drogba ya zura ma ƙasarsa ta haihuwa a wasannin na cancanta shiga gasar Afirka ta kudu. Hakazalika Didier Drogba na daga cikin yan wasa Afirka da taurarinsu ya haska a lig daban daban na nahiyar Turai. Hasali ma dai ɗaya daga cikin ƙwallaye da ya zura ne ya bai ma ƙungiyar da ya ke bugamawa wato Chelsea damar lashe kofin Ingila na bara. A ɗaya hannun kuma babbar ƙungiyar ƙwalklon kafa ta Algeriya ce CAF ta zaɓa a matsayin wacce ta fi fice a Afirka a shekara ta 2009. Yayin da Dominik Adiyiah na ƙasar Ghana ya zama gwarzon matasa yan ƙasa da shekaru 20.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halimatou Abbas