Tautaunawa da hukumar makamashi ta duniya da Iran
August 24, 2012A wannan juma'ar ne kasar Iran zata sake komawa kan teburin shawara a ci-gaba da tautaunawa da ta ke yi da hukumar makamashi ta kasa da kasa wato AIEA a kan batun shirinta na nukleya.Tun can farko dai, wata tautaunawa da a ke yi tsakanin kasar ta Iran da kuma wasu kasashe da suka hada
Amirka,Rasha,Chana,Faransa,Birtaniya da kuma Jamus sun ci karo da rashin fahimtar juna inda kasashen ke zargin hukumomin Teheran da sarrafa makaman nukleya a asirce,yayinda kasar ta dage a kan shirinta na mukamashin farar hulla ne. Wannan sabuwar masayar yayu ta zo ne a daidai lokacin da kasar Isra'ila ke yawaita barazanar kaiwa kasar ta Iran hari muddun bata dakatar da shirin nata ba.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Abdoullahi Tanko Balla