1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagogin Palestinu da Isra'ila sun kammalla taro a Amman ba tare da nasara ba

January 4, 2012

Taron kasar Jordan da ya hada yahudawa da palestinawa da kuma tawagar shiga tsakani ya watse ba tare da cimma wani sakamako ba.

https://p.dw.com/p/13dp5
Palestinian President Mahmoud Abbas (C) waves after attending an opening ceremony for the courts and research studies center in the West Bank city of Ramallah January 3, 2012. Israeli and Palestinian negotiators meet in Jordan on Tuesday alongside international mediators trying to revive their stalled peace talks, but neither side is raising hopes they can end more than a year of deadlock. REUTERS/Mohamad Torokman (WEST BANK - Tags: POLITICS)
Mahalarta taron Amman game da rikici tsakanin Isra'la da PalestinuHoto: Reuters

An watse ba tare da cimma wani sakamakon a zo a ga ni ba, tsakanin Isra'ila da Palestinu, da kuma tawagar masu shiga tsakani a taron da su ka shirya jiya a birnin Amman na kasar Jordan.

Saidai bangarorin sun yi alkwarin komawa kan tebrun shawara ranar Juma'a mai zuwa.

Tun watan satumba na shekara 2010, tattanawa tsakanin Isra'ila da Palestinu ta shiga wani halin kiki-kaka, to amma a wannan karo inji ministan harkokin wajen Jordan ,Nasser Djude an dan samu cigaba:

"Dr Erekat da sunan tawagar Palestinu ya gabatarwa Isra'ila shawarwarin warware rikicin, kuma a karon farko Isra'ila ta karbi wannan shawarwari."

Shugaban Hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya dauki matakin kauracewa shawarwarin bayan da Isra'ila da kaddamar da wasu sabin gine-gine a yankunan Palestinu.

Mawwalafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Umaru Aliyu