Taƙaddama kan kasafin kuɗin tarayyar Najeriya
August 2, 2012A wani abun dake zaman gaza kaiwa ga warware taƙaddamar dake tsakanin majalisun tarrayar Najeriya biyu da kuma ɓangaren zartarwar ƙasar an kammala wata ganawa baran baran tsakanin ministar kuɗin ƙasar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala da kuma 'yan majalisar dattawan ƙasar.
Tun ba a kai ko-ina ba dai taƙaddama ta fara ɓarkewa a tsakanin ministar kuɗin da bayan share tsawon lokaci tana wasan ɓuya da kuma 'ya'yan majlisar dattawan Najeriyar dake neman ta ruwa a jallo domin neman ba'asin gaza aiwatar da kasafin kuɗin ƙasar na bana.
Ta dai share tsawon kusan awoyi huɗu tana ƙoƙarin sauya tunanin 'yan majalisar ta kuma kai ga amsa jerin tambayoyin ya aka yi aka haife ka ga ministar da ake yiwa kirari da kafi mataimakin shugaban ƙasa da kuma majalisar ke zargi da ƙoƙarin ruɗa ƙasar kan kasafin na bana da ke ci-gaba da jawo taƙaddama a tsakanin ɓangarorin gwamnatin ƙasar biyu.
Gaza aiiwatar da kasafin kudi
Ministar dai ta ce ta ji ta gani ta kuma shaida cewar gwamnatin ƙasar ba ta da laifi ga ƙoƙarin aiwatar da kasafin da a cewar ta ke tafiya bisa ƙa'ida kuma ya kama hanyar tasiri ga makomar ƙasar ta Najeriya.
"Mun fara aiwatar da kasafin kuɗin nan a watan Afrilu wato wata huɗu da suka wuce, kuma ya zuwa yanzu da ya kamata mu saki Naira miliyan dubu 446, yanzu mun saki milliyan dubu 404, kaɗan ya gaza daga cikin wannan adadi. An yi amfani da Naira miliyan dubu 184 abun da aka yi kasafi kenan, abun da ya kamata mu saki kenan a duk wata ba mu riƙe wata dukiya ba."
Bayanan ministar ba su gamsar da 'yan majalisa ba
To sai dai kuma riƙe dukiyar ƙasa ko kuma ƙoƙarin cika ƙa'idar kasafi, daga dukkan alamu matsayin ministar ya gaza kaiwa ga burge 'yan majalisar da suka ce ba su gamsu da jerin bayanan da a cikin su ministar ta ce kasafin kuɗin ƙasar na tafiya dai dai ba.
Senator Ahmed Lawal dai na zaman ɗan majalisar dattawan Najeriyar daga jihar Yobe.
Ƙoƙarin daɗi a baka ko kuma ƙoƙarin kaucewa fushin yan majalisa dai , a baya dai tarrayar kasar ta Nigeria ta sha fama da matsalar gaza kaiwa ga aiwatar da kasafin ba tare da tada hankali a ɓangaren 'ya'yan majalisar ba.
To sai dai kuma a bana sun kai ga mancewa da banbanaci bangaranci dama jamiyyar da ta kawo su dandalin majalisar wajen tunkarar batun da kuma a cewar senator Abdul Ningi dake zaman mataimakin shugaban masu rinjayen majalisar ke da ruwa da tsaki da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.
Ana dai cigasba da ta'allaka shi kansa batun rashin tsaron dake ƙara ta'azzara cikin ƙasar da muguwar fatarar da ta yi aure tana shirin tarewa a tsakanin al'ummar ƙasar ta Najeriya a yanzu haka.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal