Taƙaddama kan shirin nukiliyar Iran
February 28, 2013Manyan ƙasashen da ke yarjejeniya da Iran sun soke wasu daga cikin sharuɗɗan da suka gindaya mata a wani yunkuri na samun maslaha ta diplomasiyya game da makamashin nukiliyarta wuni guda bayan da ɓangarorin suka kammala taronsu a ƙasar Kazakhstan.
Ƙasashen 5 da ke da kujerara dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya da Jamus yanzu sun amince Iran ta bar cibiyr inganta ma'adinin Uranium ɗinta da ke Fordo a buɗe, sai dai yanzu suna buƙatar ta rage aiki a cibiyar domin a samu damar cigaba da yarjejeniya.
Kamfanin dillancin labarun Jamus ya rawaito cewa burin ƙungiyar ƙasashen da aka fi sani da P5+1 shine Iran ta bai baiwa hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, damar gudanar da bincike a cibiyar wanda ke ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
To sai dai sun ce duk da cewa zasu barta ta sarrafa kashi 20 cikin 100 na Uranium ɗin domin samar da makamashi, ba zasu cire mata takunkumin da suka sanya mata a fannonin man fetur da kudi ba.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh