Taƙaddama tsakanin AREVA da farar hula a Nijar
December 21, 2013Talla
Dubban jama'a a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zanga-zanga a gaban cibiyar kamfanin AREVA na Faransa da ke gudanar da aikin haƙo ƙarfe uranium a yankin arewacin Nijar ɗin, domin tilasta wa kamafanin da ya ƙara yawan kuɗaɗen harajin da yake zuba wa ƙasar.
Ramatu Soli ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin farar hula da suka halarci gangamin wanda ƙungiyar ROTAB ta jagoranta. Ta ce Kamfanin ya daɗe yana cutarsu. wannan zanga- zanga na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar da ake yi tsakanin kamfannin na AREVA da hukumomin ƙasar ta Nijar,domin sake duba yarjejeniyar hako ma'addanai ke samun tsaiko.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal